Nigerian news All categories All tags
Rikicin Adamawa : An kashe kakakin jam’iyyar PDP na jihar Adamwa - PDP

Rikicin Adamawa : An kashe kakakin jam’iyyar PDP na jihar Adamwa - PDP

- Rikicin makiyaya da manoma yayi sanadiyar mutuwar mai magana da yawun bakin jam'iyyar PDP na jihar Admawa.

- Abdullahi Prembe ya ce mutuwar Zadoch babban asara ne ga jam’iyyar PDP

An kashe mai magana da yawun bakin jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP na jihar Adamawa, Sam Zadock, a ranar Talata.

Sam Zadock yana cikin mutane goma sha uku da aka kashe a jihar Adamawa yayin da rikici ya barke tsakanin makiyaya da manoma a jihar.

Rikicin Adamawa : An kashe kakakin jam’iyyar PDP na jihar Adamwa - PDP

Rikicin Adamawa : An kashe kakakin jam’iyyar PDP na jihar Adamwa - PDP

A ranar Laraba jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar, Mista Sam Zadoch ta sanadiyar rikici da ya barke tsakanin ‘yan tawayen kabilar Bachama da makiyaya a yankin Numan Demse a ranar Talata.

KU KARANTA : Kwastam ta kwace motoci 177 iyakar Legas

Da yake magana a ranar Laraba, Sakatren PDP na jihar Adamawa, Abdullahi Prembe, ya ce mutuwar Zadoch Babban asara ne ga jam’iyyar su.

“Wannan dalilin yasa muke ta kira da gwamnatin tarayya ta gaggauta kawo karshen rikicin makiyaya da manoma da ya addabi wasu yankunan kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel