A daina yi wa jarirai wanka da ruwan zafi da zaran an haihu - Helen Bulu
- Helen Bulu ta ce yiwa jarirai wanka daruwan zafi da zaran an haife su bashi da kyau
- Bulu ta ce duk wani zafi da jariri ya ke da bukata ya same shi a cikin mahaifiyar sa
Wata kwararriya akan harkan kiwon lafiya, Helen Bulu, ta gargadi iyaye mata a Najeriya da su dain yi wa sabbin jarirai wanka da ruwan zafi da zarar an haife su da kuma al’adar fizgar hannu da kafafun su da ake yi da nufin yi musu mika.
Helen Buna ta bayyaan haka ne a taron wayar da iyaye mata muhimmacin yiwa ‘yayan su allurer rigakafi da aka yi a makon da ta gabata a brining Abuja
Bulu ta ce yi wa yara wanka da ruwan zafi tare da ja wa jariri hannaye da kafafu da akeyi lokacin da aka haihu na illata lafiyar jariri.
Ta kara da cewa “Duk wani d, saboda haka babu wani karuwa da jariri yake samu daga yi masa wanka da ruwan zafi sai da ma yayi masa illa".
KU KARANTA : Shugaba Buhari ya baiwa jahohin Najeriya bashin Naira 1.9 tiriliyan daga asusun rarar man fetur
Helen ta ce, turawa basa yiwa ‘ya’yansu wanka da ruwan zafi da zarar an haife su kuma basa musu mika amma yaransu na tashi cikin koshin lafiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng