Gwamnati za ta kafa kwamitin bincike kan yadda aka sace ‘yan matan Dapchi

Gwamnati za ta kafa kwamitin bincike kan yadda aka sace ‘yan matan Dapchi

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa gwamnatin tarayya za ta kafa kwamitin mutane 12 domin bincikar yadda aka sace yan matan makarantar sakandare dake garin Dapchi a jihar Yobe.

Gwamnatin zata kaddamar da wannan kwamiti ne a yau Laraba, 28 ga watan Fabrairu, wanda mambobinta zasu hada da sojoji, yan sanda da kuma hukumar SSS.

Ayyukan da kwamitin za ta gudanar sun hada da bincikar dalilan da ke tattare da sace wadannan ‘yan mata.

Haka zalika kwamitin zata yi duba ga yadda jami’an tsaro ke gudanar da ayyukansu a Dapchi da kuma makarantar kafin sace daliban.

Gwamnati za ta kafa kwamitin binciko yadda aka sace ‘yan matan Dapci
Gwamnati za ta kafa kwamitin binciko yadda aka sace ‘yan matan Dapci

Daga karshe ana sanya ran kwamitin zata gabatar da shawarwari da za’ayi amfani da su wajen gano inda aka kai ‘yan matan da kuma yadda za’a ceto su.

KU KARANTA KUMA: Babban magana: Ana shirin maka Ganduje a kotu

Gwamnati za ta baiwa kwamitin zuwa ranar 15 ga watan Maris na 2018 ta gabatar da bayanan da ya tattara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel