Wajibi ne mu yi nasara a zaben Ekiti da Osun a shekaran nan - Oyegun

Wajibi ne mu yi nasara a zaben Ekiti da Osun a shekaran nan - Oyegun

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), John Odigie-Oyegun, y ace jam’iyyar zata yi duk abinda ke yiwuwa domin lashe zaben gwamnan jihar Ekiti da Osun da za’a gudanar a wannan shekaran.

Yayinda yake jawabi a taron ganawar masu ruwa da tsaki da aka yi a sakatariyan jam’iyyar jiya Talata, Mr Oyegun ya ce yanada matukar muhimmanci jam’iyyar ta lashe zaben a wadannan jihohi saboda shine madubin abinda ka iya faruwa a shekarar 2019.

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta shirya gudanar da zaben jihar Ekiti ranan 14 ga watan Yuli, na jihar Osun kuma ranan 22 ga watan Satumba, 2018.

Wajibi ne mu yi nasara a zaben Ekiti da Osun a shekaran nan - Oyegun
Wajibi ne mu yi nasara a zaben Ekiti da Osun a shekaran nan - Oyegun

Yace: “Ina son mika godiyata ga abokan aikina, shugabannin jam’iyya a jihohi da gudunmuwar da suke badawa duk da kalubalen da muke fuskanta.”

“Wadannan zabububakan ne maduban zaben kasa ga baki daya. Saboda haka wajibi ne mu daukesu da muhammanci saboda wadannan zabe ne wanda sai inda karfinmu ya kare.”

KU KARANTA: Rauni zai hana Neymar karawa da Ronaldo na Madrid

Santoci 2, mambobin majalisa 3 ne suka wakilci kowani yanki, shugbannin jam’iyyar a jihohi 36 da kuma shugabannin jam’iyyar ta kasa ne suka halarci taron.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng