Masu garkuwa da mutane 3 da Soja 1 sun mutu a yayin wani musayar wuta da suka yi da juna
Rundunar Sojan kasa ta Najeriya ta tabbatar da mutuwar wasu masu garkuwa da mutane guda uku, tare da Soja guda daya a garin Okene na jihar Kogi, inji rahoton kamfanin dillancin labaru,NAN.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Talata 27 ga watan Feburairu, a yayin wani musayar wuta da Sojojin suka yi da barayin, da nufin ceto wani attajiri da suka sace.
KU KARANTA: Sanata Abdullahi Adamu ya bukaci masu yiwa gwamnatin Shugaba Buhari zagon kasa dasu fice daga jam'iyyar APC
Kaakakin runduanr Sojan dake jibge a jihar Kogi, Kyaftin Weri Finikumor ya bayyana ma majiyarmu cewa sun samu nasarar kama wasu daga cikin barayin, kuma a yanzu haka suna basu hadin kai ta hanyar basu bayann sirri.
Rahotanni sun tabbatar da cewar Sojojin sun yi kokarin kwato Alhaji Momoh Otinau ne, wani hamshakin attajir da barayin suka sace shi a ranar 17 ga watan Feburairu, lokacin da yake tare da abokansa a gaban wani Masallci.
Wani dan uwan Momon da barayin ke tattauna yiwuwar biyan kudin fansa da shi ne ya fara fada ma Sojoji niyyarsa na zuwa ajiye ma barayin kudin fansar da suka bukata a inda suka bukata, wannan ne ya sanya Sojojin suka raka shi.
Amma daga hango su, sai barayin suka bude musu wuta, inda su ma Sojojin suka mayar da wuta, nan fa aka yi kare jinni, biri jini, inda Sojoji suka kashe barayin guda uku, su kuma suka yi asarar Soja daya, a yanzu an mika gawar Sojan dakin ajiyan gawawwaki.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng