Kasar Amurka na neman Shugaban Boko Haram Abu Musab Al-Barnawi
- Amurka ta sa Abu Musab Al-Barnawi cikin manyan ‘Yan ta’adda
- Kasar ta Amurka dai tana kokain ganin bayan ta’addanci a Duniya
- Ana ta kokarin murkushe Kungiyar manyan ‘Yan ta’adda ta ISIS
Kasar Amurka ta sa wani ‘Yan Najeriya cikin sahun manyan ‘Yan ta’addan da ta ke nema yanzu ruwa-a-jallo a Duniya. Bayan nan kuma an sa wasu kungiyoyin Duniya 7 a jan layi yanzu.
Hukumar da ke kula da harkokin tsaro a Amurka ta sa Shugaban Kungiyar wani bangare na Boko Haram watau Abu Musab Al-Barnawi cikin manyan ‘Yan ta’addan da ta ke nema a Duniya. Yanzu haka Al-Barnawi yana kan gaba a shafin Kasar.
KU KARANTA: DSS ta damke wadanda su ka kashe wani 'Dan Majalisa
Bayan Shugaban na Boko Haram, Kasar ta Amurka ta na neman Mahad Moalim na kasar Somalia ido rufe. Akwai wasu Kungiyoyi 7 na Duniya a Kasashen Somaliya, Tunisiya, Masar da Najeriya da sauran su da ake kokarin takawa burki.
Damke wadannan mutane na cikin hanyoyin samun nasara wajen kawo karshen ta’addancin ISIS a Duniya. Amurka na ganin hakan zai hana ‘Yan ta’addan ISIS daukar hayan Sojoji a sauran kashen Duniya irin su Najeriya da Somaliya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng