Kurungus! Uwar jam’iyyar APC ta rabar gardama game da rikicin shugabancin APC a Kaduna

Kurungus! Uwar jam’iyyar APC ta rabar gardama game da rikicin shugabancin APC a Kaduna

Karshen tika tika tik, inji Hausawa, daga karshe dai gaskiya ta yi halinta a jihar Kaduna, inda aka sha fama tsakanin tsagin jam’iyyar APC akida da kuma tsagin gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Elrufai game da shugabancin jam’iyyar.

Dukkanin bangarorin biyu na ikirarin cewar sune halsatattun yayan jam’iyyar a Kaduna, don haka su ne masu halartaccen shugaban jam’iyyar a jihar, wanda hakan ta kai ga kowanne bangare na sallamar jiga jigan bangaren da yake takun saka da shi.

KU KARANTA: Sanata Abdullahi Adamu ya bukaci masu yiwa gwamnatin Shugaba Buhari zagon kasa dasu fice daga jam'iyyar APC

Legit.ng ta ruwaito alamu sun tabbatar da cewar uwar jam’iyyar APC ta fi gamsuwa da shugaban tsagin APC na gwamnan jihar Kaduna, wato Alhaji Shuaibu Idris Lauje, kamar yadda Kaakakin gwamnatin jihar Samuel Aruwan ya tabbatar a shafinsa na Facebook.

Kurungus! Uwar jam’iyyar APC ta rabar gardama game da rikicin shugabancin APC a Kaduna
Shuaibu

Samuel ya daura hotunan Alhaji Shuiabu ne a farfajiyar ofishin jam’iyyar APC bayan kammala taron masu ruwa da tsaki, jigogi, da kuma masu fada a ji na jam’iyyar, wanda ya gudana babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata 27 ga watan Feburairu.

Idan za’a tuna kimanin sati biyu kenan suka gabata, tun bayan da tsagin APC Akida da ya kunshi Sanata Shehu Sani, Sanata Hunkuyi, Dakta Hakeem Baba Ahmed, Tijjani Ramalan da sauransu sun dakatar da Gwamna El-Rufai daga jam’iyyar a ranar da suka bude sabob ofishinsu, sai dai gwamnatin ta ruwa gidan a washegari.

Kurungus! Uwar jam’iyyar APC ta rabar gardama game da rikicin shugabancin APC a Kaduna
Shuaibu

Haka zalika shi ma Sanata Shehu Sani ya sha samun takardar dakatarwa da ma na sallama daga jam’iyyar APC tsagin gwmanatin jihar, dake fitowa daga shuwagabannin mazabarsa ta Tudun wada Kaduna.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng