Rundunar Sojin Najeriya sun aika Makiyaya 10 lahira a wani Kauye
- An yi musayar wuta tsakanin Sojoji da wasu Makiyaya a Numan
- Makiyayan sun kona gidajen jama’a a wani Kauye a cikin Garin
- Janar Texax Chukwu yace Sojojin sa sun takawa Makiyayan burki
Dakarun Sojojin Exercise Ayem Akpatuma da aka tura domin kawo karshen rikicin Makiyaya sun fara aiki kuma har sun damke wasu Makiyaya da su ka kona wani gari a cikin Jihar Adamawa. Tuni Sojoji su kayi ram da wadannan Makiyaya.
Bataliyar Sojojin Operation Cat Race da aka aika Garin Numan a cikin Jihar Adamawa sun agazawa wata Runduna inda su ka ceci mutanen Garin Gwamba da Makiyaya su ka tasa a gaba har su ka kona gidaje rututu a jiya Talata.
KU KARANTA: An kashe wasu manyan Sojojin Boko Haram
Makiyayan sun kona gidaje da dama na Jama’a a Kauyen na Gwamba kafin Dakarun Najeriya su kawo dauki. Ana zargin Makiyaya sun kashe wasu daga cikin mutanen Garin a harin da su ka kai kafin Jami’an tsaro su isa wurin.
Sojojin kasar sun kama mutane 6 yayin da su ke kokarin tserewa a wani kauye mai suna Garigiji. An kuma kashe Makiyaya kimanin 10 bayan musayar wuta sannan an karbe makamai na bindigogin Ak-47 da sauran su a hannun Makiyayan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng