Tofa: Makiyaya sun shiga Jihar Benuwe sun kori kowa a Garin

Tofa: Makiyaya sun shiga Jihar Benuwe sun kori kowa a Garin

- Makiyaya sun kori kaf Jama’a daga wani Gari a Benuwe

- Ba a kashe kowa ba dai a wannan harin da aka kai jiya

- Makiyayan dai su na neman inda za su samu ciyawa ne

Makiyaya sun kara yin wata barna a Yankin Chili da ke cikin Garin Mbatoho a Karamar Hukumar Makurdi ta Jihar Benuwe. Yanzu haka an fatattaki mutanen Garin kamar yadda mu ke ji. Gwamnatin Jihar dai ta soma bincike.

New Telegraph ta rahoto cewa wasu Makiyaya sun shiga Mbatoho inda su ka nemi jama’a su fice daga Garin a Ranar Talatar nan. John Terhemen wanda shi ne Shugaban mutanen Yankin ya bayyanawa Hukuma abin da ya faru.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga sun sace wani Basarake a Jihar Taraba

John Terhemen ya jagoranci jama’a zuwa ofishin Mataimakin Gwamnan Jihar Benuwe Injiniya Benson Abounou inda ya masa bayanin yadda su ka kwashe da Makiyayan wanda su ka kora su domin su ba dabbobin su abinci a Garin.

Wannan mutumi ya bayyana cewa Makiyayan ba su taba kowa ba kuma ba a kona gida ko guda ba sai dai an nemi kowa ya bar garin domin su ba shanun su ciyawa. Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Benuwen shi ma ya tabattar da wannan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng