Ka da mu sake jin an sace 'Yan Makaranta - 'Yan Majalisa sun fadawa Shugaban kasa
- Majalisa ta nemi Gwamnati ta kawo karshen barnar Boko Haram
- Kwanan nan aka zargin Kungiyar da satar wasu 'Yan makaranta
- Dan Majalisar Yankin yace mutanen Yobe na fuskantar barazana
Labarin da mu ke ji daga 'Yan jarida shi ne 'Yan Majalisun Tarayya sun ja kunnen Gwamnatin Tarayya inda su ka fadawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsare 'Yan makaranta da ke Yankin Arewa-maso-gabashin kasar.
Majalisar Wakilan Najeriya ta nada wani kwamiti domin ziyartar Garin Dapchi domin ganewa kan su game da satar 'Yan Makaranta sama da 100 da aka yi a Yankin bayan wani 'Dan Majalisar Jihar Yobe ya kawo maganar a zaman jiya.
KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun ceto mutane sama da 1000
Honarabul Goni Lawan (APC, Yobe) ya bayyanawa Majalisar cewa a 2014, an taba yanka 'yan Makarantar koyon harkar noma sama da 50 a Garin Buni-Yadi da ke cikin Jihar. 'Dan Majalisar yace 'yan ta'adda nayi wa mutanen Yankin illa.
Don haka ne Dan Majalisar na Jihar Yobe yace dole Gwamnatin Tarayya ta kawo karshen aukuwar wannan mummunan abu a fadin Arewa-maso-gabashin kasar. Yanzu haka dai babu Sojoji a wasu Yankin don haka ake samun baraka.
Majalisar dai ta yanke shawarar cewa ya kamata Gwamnati ta aika Rundunar Sojojin sama da na kasa da kuma jami'an tsaro na farar hula domin ganin an ceto 'Yan Makarantar da aka sace a Garin Dapchi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng