Dandalin Kannywood: Rahama Sadau ta yi juyayi akan mutuwar Sridevi
Shahararriyar jaruman nan ta kamfanin shirya fina-finan Hausa da na Kudu, Rahama Sadau ta bi sahun jaruman duniya gurin nuna alhininsu akan mutuwar jarumar kasar Indiya Sridevi.
Jaruma Sridevi ta mutu ne a kasar Dubai, bayan ta halarci wani bikin aure.
Sridevi ta yi suna a harkar finai-finai ne tun bayan fitowa da tayi a wani babbar fim mai suna Mr. India.
Jaruma Rahama Sadau ta yi ta saka hotunan ta da bidiyo a shafinta na Instagram domin nuna alhini kan mutuwar ta.
KU KARANTA KUMA: An zuba matakan tsaro a sakatariyar APC yayinda ake gudanar da babban taro
Daga cikin wadanda suka jajanta wa iyalan mamaciyar sun hada da firam ministan kasar Indiya, da jaruman duniya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng