Dapchi: Karka biya kudin pansa: Hukumomi sun shawarci shugaba Buhari

Dapchi: Karka biya kudin pansa: Hukumomi sun shawarci shugaba Buhari

- Wasu kungiyoyi masu zaman kansu a Najeriya suna tunanin masu tallafa wa kungiyar Boko Haram suna kokarin ganin Najeriya ta rabe

- Kungiyoyin sun bukaci gwamnatin tarayya ta guji biyan kudaden fansa ga kungiyar ta Boko Haram don ceto yammatan 110 da aka sace a Dapchi

- Kungiyoyin suna son a tabbatar cewa dakarun sojojin Najeriya ne za su ceto yaran kuma su mayar da su zuwa ga iyayen su

Kimanin kungiyoyin sa kai guda hamsin ne suka bukaci gwamnatin tarayya ta guji biyan kudin fansa ga yan kungiyan Boko Haram don ceto yan matan sakandire 110 da ake zargin kungiyar ne ta sace daga makarantar sakandire na Dapchi da jihar Yobe.

Dapchi: Karka biya kudin pansa: Hukumomi sun shawarci shugaba Buhari
Dapchi: Karka biya kudin pansa: Hukumomi sun shawarci shugaba Buhari

Kungiyoyin sunyi magana ne a wata taro da sukayi ranar Litinin 26 ga watan Fabrairu a garin Abuja inda suka bayyana cewa biyan kudi ko kuma yin sulhu da kungiyar zai kara musu kwarin gwuiwa ne.

DUBA WANNAN: Dakurun soji sun ceto mutane 1,127 daga hannun Boko Haram - Hukumar Sojin Najeriya

Kungiyoyin sunyi ikirarin cewa wasu yan kasashen waje ne ke hada baki da wasu daga cikin yan kungiyar ta Boko Haram don kulla makircin da zai janyo rabewar Najeriya.

"A ranar Litinin 19 ga watan Fabrairun 2018, kimanin dalibai 105 ne wasu yan bindiga da ake kyautata zaton yan Boko Haram ne suka sace daga makarantar sakandiren yan mata da Dapchi na jihar Yobe," inji Kungiyoyin

"Niyyar su shine su gusar da dukkan kokarin da gwamnati tayi wajen kawar da ta'addanji a kasar nan.

"Ya zama dole gwamnati ta guji biyan kudin fansa domin ceto yan matan domin bayanan da muka samu shine yan kungiyar sunyi odar makamai kuma suna jiran kudin ne suyi amfani dashi.

"Muna kira da da sojojin Najeriya su dage wajen ceto yan matan kana hukumomin tara bayanan sirri suyi kokari wajen gano wandanda ke tallafawa mayakan Boko Haram din,"

A wani rahoton kuma, Legit.ng ta kawo muku rahoto inda jam'iyyar PDP ta bukaci majalisar kasa ta fara gudanar da bincike don gano yadda akayi har yan ta'addan suka sace mata daga makarantar na Dapchi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164