Siyasar Kaduna: Za mu ba mata fom din takara kyauta – Jam’iyyar PDP

Siyasar Kaduna: Za mu ba mata fom din takara kyauta – Jam’iyyar PDP

Rahotanni sun kawo cewa babban jam’iyyar adawa ta kasa wato PDP tayi alkawarin ba duk macen da za tayi takarar kujeran kansila da na shugaban karamar Hukuma a zaben kananan hukumomi mai zuwa da za a yi a Kaduna fom kyauta.

A cewar jam’iyyar duk mai neman takarar kansila zai siya fom din nuna son yin takara naira N5000 sannan kudin fom naira N30,000.

Ciyaman kuma zai siya fom din nuna son yin takara naira N25,000 sannan kudin fom kuma N100,000.

Hukumar zabe na Jihar Kaduna ta tsaida ranar 12 ga watan Mayu domin gudanar da Zaben kananan hukumomi a Jihar.

Siyasar Kaduna: Za mu ba mata fom din takara kyauta – Jam’iyyar PDP
Siyasar Kaduna: Za mu ba mata fom din takara kyauta – Jam’iyyar PDP

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa yayinda jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta fara taron ta na kasa a Abuja a ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu, rahotanni sun kawo cewa hedkwatar jam’iyyar na cike da jami’an tsaro.

KU KARANTA KUMA: An zuba matakan tsaro a sakatariyar APC yayinda ake gudanar da babban taro

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa da misalin karfe 6 na safe, manyan motoci na sojoji da yan sanda suka kewaye wajen da kuma wajen shiga da fita unguwar Blantyre, inda sakatariyar jam’iyyar yake.

Rahoton ya kawo cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da gwamnonin APC 24 zasu halarci taron.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: