EFCC ta kama wani ma'aikacin banki da ya karkatar da N700m daga asusun masu ajiya

EFCC ta kama wani ma'aikacin banki da ya karkatar da N700m daga asusun masu ajiya

- Hukumar EFCC ta gurfanar da wani tsohon ma'aikacin banki a gaban kotu bisa tuhumar sa da karkatar da kudaden al'umma har N700m

- EFCC ta ce tsohon ma'aikacin ya hada baki da wasu mutanen ne inda ya karkatar da kudaden zuwa asusun ajiyar sa da ke wasu bankunan daban

- Wanda ake tuhuma ya musanta aikata laifin, hakan yasa alkali ya ce a cigaba da tsare shi a gidan kurkuku har zuwa rannan da za'a fara sauraron karar a wata mai zuwa

Hukumar yaki ta masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'anati (EFCC) ta gurfanar da wani ma'aikacin banki, Nsa Ayi a gaban wata babban kotu da ke Ikeja a Legas bisa tuhumar sa da karkatar da kudaden masu ajiya har Naira miliyan dari bakwai.

EFCC ta kama wani ma'aikacin banki da ya karkatar da N700m daga asusun masu ajiya
EFCC ta kama wani ma'aikacin banki da ya karkatar da N700m daga asusun masu ajiya

A karar da EFCC ta shigar gaban Alkali Mojisola Dada na baban kotun, ta kuma tuhume Ayi da laifin kwaikwayon san hannun wasu masu ajiya a bankin sannan ya tura kudaden nasu zuwa wasu asusun ajiyar sa da ke wasu bankunan.

DUBA WANNAN: EFCC ta titsiye Stella Oduah na tsawon sa'o'i goma a kan badakalar N9.4bn

Hakan yasa EFCC ke tuhumar sa da aikata laifka 11 masu nasaba da damfara wanda sun sabawa sashi 335(a) na dokar masu laifi na jihar Legas na shekarar 2011.

Wanda ake tuhumar da tsohon ma'aikacin wata banki ne mai suna 'Coronation Merchant Bank' kuma ana zargin ya hada baki da wasu ne wajen karkatar da kudaden al'umma masu niyyar siyar hanayen jari daga gwamnatin tarayya, kuma ya tura kudaden zuwa asusun ajiyar sa na bankin Zenith 1002771899 da Guaranty Trust Bank 0001600855.

Sai dai bayan kotu ta karanto masa laifukan da ake tuhumar sa da aikatawa, ya amsa da cewa bai aikata laifukan ba. Ayi ya kuma roki kotu ta bashi damar tafiya kasan wajen don ya kai yaron sa asibiti amma kotun bata amince ba saboda a takardan neman izinin an gano cewa dukkan iyalan nasa ya ke son tafiya dasu kuma akwai yiwuwar idan ya tafi ba zai dawo ba.

Kotu ta bayar da umurnin a cigaba da tsare shi a gidan kurkuku na kiri-kiri har sai rannanakun 6, 26, 29 na Mayu da kuma 16 da 27 na Afrilu da za'a cigaba da sauraron karar na sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164