Rundunar soji sun kama mutane 9 dake da hannu a kisan marigayi dan majalisa Hosea Ibi (hotuna)
Rundunar Birgediya 23 da aka kai Wukari da tawagar hukumar DSS daga Jalingo sun gudanar da wani gagarumin bincike a tsakanin Takum a ranar Asabar 24 ga watan Fabrairu.
A lokacin binciken an kama mutane uku da ake zargi da garkuwa tare da kashe Hosea Ibi, wani dan majalisar dokokin jihar Taraba da kuma Mista Chidiebere wanda aka saka bayan an biya kudin fansa.
Wadanda aka kama sune Jaka Ejukun (shekara 24), Peter Isaga (shekara 33) da kuma Arachukwu Bedforth (shekara 21).
Bayan haka an sake gudanar da bincike a ranar 25 ga watan Fabrairu a Gbise, karamar hukumar Kastina Ala inda aka kara kama wasu mutanen. An kama su ne a gurare daban-daban.
Wadanda aka kara kamawa sune Isaiah Suwe (shekara 23) dan kabilar Tiv daga karamar hukumar Lessel Ushongo, Amadu Barnarbas Torva (Atamanin) (shekara 23) daga karamar hukumar Gbise Kastina Ala, Aondi Teroo (shekara 21), Nengenen Mbaawuaga Damian (shekara 22), Aondoase Kayitor (shekara 18) da kuma Ternenge Tersoo (shekara 19).
Daya daga cikin masu laifin Amadu Barnabas Torva na da hannu dumu-dumu a kisan Hosea Ibi. An kuma same su da layukan waya, katin ATM, katin zabensa da sauran abubuwa.
KU KARANTA KUMA: Dandalin Kannywood: Jarumai ma’aurata da suka kafa tarihi tare da nuna kaunar da suke ma juna (hotuna)
A yanzu haka suna hannun hukumar DSS inda suke amsa tambayoyi.
A baya Legit.ng ta kawo cewa Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku, ya umurci jami’an tsaro a jihar da su tsamo wadanda suka kashe dan majalisa mai wakiltanmazabar Takum 1, a majalisar dokokin jihar Taraba, mai girma Hosae Ibi.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng