Kundin tarihi: Hotunan masarautar Borno da sarakunan ta na shekaranjiya, jiya da yau
Masarautar Borno, da aka fi sani da Daular Elkanemi, na daga cikin tsofin masarautu da suka dade da kafuwa a nahiyar Afrika.
Masana tarihi sun tabbatar da cewar masarautar Borno ta kafu tun kafin karni na 10, tun kafin zuwan addinin musulunci.
Daular Borno ta samo sunan Daular Elkanemi ne daga sarkin Daular, Muhammad al-Amin Elkanemi, mutumin da kawo karshen mulkin Saifuwa da su ka shafe tsawon shekaru 800 su na rike da shi. Elkanemi ya hambarar da mulkin Saifuwa ne a karni na 18, kamar yadda jaridar BBC Hausa ta wallafa tarihin masarautar.
DUBA WANNAN: Jerin makamai 9 da hukumar 'yan sanda ta haramta amfani da su
Kafin mulkin mallaka, Daular Borno, ta yi mamayar garuruwa da suka hada wasu garuruwa da yanzu ke cikin Nijar, Chadi, Kamaru, Sudan, har da Libiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng