Bayan yan fashi sun ji mata rauni, mata mai juna biyu ta cika a asibiti bayan haihuwa

Bayan yan fashi sun ji mata rauni, mata mai juna biyu ta cika a asibiti bayan haihuwa

Wata mata mai juna cewa ta rigamu gidan gaskiya bayan ta haihu bayan yan fashi sun saceta a Badagry na jihar Legas.

Duk da cewan ta haihu a wani aikin Tiyata a asibiti, ta mutu ne sanadiyar raunuka da ta samu sakamakon harin.

An samu rahoton cewa matan na dauke da kaya a mota mai lamba KTU 356 CE na dauke da fasinjoji daga garin Kwatano, jihar Benin zuwa Legas.

Matan ta yi tunanin cewa motan haya ne kawai sai suka fito da makamai kuma suka kwace dukiyoyinta.

Yayinda suke tafiya da ita, sai ta fara iwu a cikin motan. Da jama’a suka gano su, sai aka fara binsu a baya.

Bayan yan fashi sun ji mata rauni, mata mai juna biyu ta cika a asibiti bayan haihuwa
Bayan yan fashi sun ji mata rauni, mata mai juna biyu ta cika a asibiti bayan haihuwa

Dubunsu ya cika yayinda jami’an FRSC suka taresu a kan hanya. Jami’an yace:

“Mun tare mota kuma munga suna kokarin toshe bakin matan da ke iwi. Sunyi niyya jefar da ita daga cikin mota amma suka kasa saboda motocin da ke binsu a baya.

“Mun lura cewa ta ji rauni sai muka kai ta asibiti inda ta haihu cikin mintuna 20.

“Amma kafin mu dawo, sai muka ga jama’a sun hau kansu da duka suna kokarin banka musu wuta. Sai wasu jami’an soji suka cecesu daga hannun jama’a suka mikasu ga yan sanda.”

KU KARANTA: Makiyaya sun tashi dan mallakar katin zabe

Misalin karfe 3 na ranan, hukumar ta samu labarin cewa matan ta cika kuma an ajiye gawarta a dakin ajiye gawawwakim asibitin Badagry.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng