Dubun yan fashi 13 da suka addabi garin Suleja ya cika

Dubun yan fashi 13 da suka addabi garin Suleja ya cika

Hukumar yan sandan jihar Neja ta cika hannu da wani yan fashi 13 da suka addabi garin Suleja da kewaye.

Yan fashin sun yiwa masu abubuwan hawa a hanyan Suleja inda suka kwace dukoyoyin mutane.

Allah ya tona musu asiri ne yayinda suka yiwa wani mai suna Tauheed Isyaki fashi a unguwan Lambata na karamar hukumar Gurara inda suka kwace masa wayoyi. Kawai sai ya sanar da jami’an hukumar yan sanda da ke hanyan.

Kakakin hukumar ya bayyanawa yan jarida cewa an damkesu a wurare daban-daban a jihar.

Dubun yan fashi 13 da suka addabi garin Suleja ya cika
Dubun yan fashi 13 da suka addabi garin Suleja ya cika

Yan fashin sune ; Saidu Kabiru, 21; Abubakar Sadiq, 22; Usman Ali, 20; Bala Abdullahi, 28; Lukman Abubakar, 25; Mohammed Mohammed, 21, and Hussaini Ibrahim, 21, Zaharadeen Adam, 19; Abdullahi Yahaya, 22; Aliyu Sani, 21; Abubakar Shehu, 20; Hassan Ibrahim, 21, da Abdulmalik Usman, 22.

KU KARANTA: Makiyaya sun tashi dan mallakar katin zabe

Hukumar yan sandan jihar ta alanta fito-na-fito da masu tayar da zane tsaye a fadin jihar. Suna kira da al’umma su taimaka wajen kawo kara ofishin yan sanda mafi kusa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng