Tsabar kyau da Allah ya yi mani na neman hana ni zaman aure - Fatima Mohammed ta shaidawa kotu
Wata mata mai suna Fatima Mohammad mai shekaru akalla 16 a duniya ta shaidawa wata kotun da ke zama a Abuja yadda tsananin kyaunta ke hana ta zaman lafiya da mijinta mai suna Tasi'u Kasim da suka shafe shekaru biyu tare.
Matar, Fatima Mohammad dai ta doshi kotun ne sannan kuma ta roke ta da ta taimake ta ta raba auren nasu don kuwa a cewar ta tuni zaman lafiya yayi kaura a tare da ita da mijinta.
KU KARANTA: An gano inda rabin 'yan matan Dapchi suke
Legit.ng ta samu cewa Fatima ta: "Mijin nawa yana bugu na kamar kurar bara kuma sannan baya kura da hakkoki na na zamantake wa ko kadan. Haka zalika saboda ina da matukar kyau, yanzu kullum cikin zargi na yake da cewa mazan waje na nema na" ta ci gaba da cewa.
A wani labarin kuma, daga majiyar mu ta Punch na nuni da cewa wani bakanike mai gyaran tayar mota a garin Mbiabam Ibiono na karamar hukumar Ibiono Ibom a jihar Akwa Ibom mai suna Nkere Uta ta make matar sa mai suna Bella Uta har lahira a jiya Litinin.
Kamar dai yadda muka samu, ma'auratan da suka shafe shekaru da yawa a tare suna da 'ya'ya biyar kafin aukuwar lamarin da yayi matukar girgiza al'ummar yankin.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng