Rikicin El-Rufai da sauran ‘Yan Jam’iyya a Kaduna na iya kawowa APC cikas a 2019
- Ana rigima tsakanin wasu jiga-jigan APC a cikin Jihar Kaduna
- Wasu sun fara kira ga Aminu Abdulfatah ya fito takara a 2019
- Ana ganin tsohon kakakin Majalisar zai iya kawo gyara a APC
Mun samu labari daga Jaridar Leadership cewa wasu manyan ‘Yan APC a Jihar Kaduna sun fara ganin cewa takkadamar Gwamnan Jihar da wasu ‘Yan Jam’iyyar na iya jefa APC cikin matsala.
Wani babba a Jam’iyyar APC ta Jihar Kaduna mai suna Alhaji Danazumi Mai Lambu yayi kira ga ‘Ya ‘yan Jam’iyyar da ke rikici da su bi a hankali kara koma gidan jiya bayan irin kokarin da Gwamnatin APC da Gwamnatin Shugaba Buhari tayi.
KU KARANTA: Atiku Abubakar ya karyata Gwamnatin Buhari
Babban jigon na Jam’iyyar mai mulki yayi kira ga tsohon Kakakin Majalisar dokokin Jihar Kaduna watau Aminu Abdulfatah ya fito takarar Gwamnan Jihar ta Kaduna don kuwa shi kadai ne zai iya gyara Jihar saboda kwarewar sa da dattaku da sanin aiki.
‘Dan siyasar yana ganin cewa Abdulfatah zai iya maganin rikicin da ke cikin Jam’iyyar har ma ya jawo wasu ‘Yan adawa zuwa APC idan ya samu mulki. Ya kuma ce wannan Gwamnatin ta Shugaba Buhari tayi bakin kokari kuma tana kan yi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng