Har yanzu babu labarin ‘Yan Makarantar da aka sace a Garin Dapchi
- Tun kwanaki aka sace yaran makaranta a cikin Garin Dapchia
- Har yanzu babu labarin inda aka shiga da wadannan ‘Yan mata
- ‘Yan Boko Haram dai da su ka saba satar yara ba su ce komai ba
Kawo yanzu da mu ke magana, babu wani bayanin kirki game da ‘Yan matan Makarantar da aka sace a Makarantar Gwamnatin mata da ke Garin Dapchi a Jihar Yobe cikin ‘yan kwanakin nan.
Kamar yadda rahotanni ke zuwa mana, har yanzu ba a gano ‘Yan makarantar Dapchi da aka sace ba. Tawagar Al-Barnawi na ‘Yan Boko Haram da su ka saba satar ‘Yan mata har yanzu ba su ce komai ba game da wannan hari.
KU KARANTA: Sojoji sun hana rikici ya barke a Yankin Arewa
Yanzu dai Jaridar Daily Trust tace zaman dar-dare ake yi a Garin na Dapchi inda sama da mata 100 su ka fada hannun ‘Yan ta’addan Boko Haram a Ranar 19 watannan. Iyayen yaran da aka sace dai yanzu ba su iya barci inji majiyar mu.
Masana harkar tsaro su na ganin cewa an sace yarar ne saboda samun hanyar kudi kamar yadda ‘Yan ta’addan su ka saba. Wata majiyar na cewa har an shiga da yaran zuwa inda ake boye su yayin da Jami’an tsaro ke cigaba da aiki.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng