Gwamnatin Kasar Saudiyya ta bawa mata damar shiga aikin soja

Gwamnatin Kasar Saudiyya ta bawa mata damar shiga aikin soja

- Wannan dai shine kusan karo na biyu da gwamnatin kasar saudiyya ta bawa mata damar shiga aikin soja.

- Hukumar tsaron kasar ta bukaci mata masu sha'awar aikin sojan da su kai takardun su

- Hakan kaman wani sabon abu ne a tsarin gwamnatin kasar

Gwamnatin Kasar Saudiyya ta bawa mata damar shiga aikin soja
Gwamnatin Kasar Saudiyya ta bawa mata damar shiga aikin soja

A karo na biyu kenan kasar Saudiyya inda kasar ta bawa mata damar shiga aikin soja.

Hukumar tsaro ta kasar Saudiyya ta bukaci mata wadanda suke da burin shiga aikin soja da su tura takardun su ta yanar gizo domin neman shiga aikin.

DUBA WANNAN: An fara shan kidan Jazz a Saudiyya

Hukumar ta ce zata cigaba da karbar takardun matan masu sha'awar shiga aikin har nan da ranar Alhamis 1 ga watan Mayu.

A makon daya gabata ne ofishin bayar da fasfo na kasar Saudiyya ya bukaci mata masu bukatar shiga aikin lura da kan iyakoki a filin jirgin sama dasu gabatar da takardun su.

A kasar Saudiyyan ana ta fito da sabbin sauye sauye a bangaren raya al'adu, zamantakewa da tattalin arziki wanda Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman ke gabatarwa.

Kasashe da dama suna ganin hakan a matsayin sabon al'amari a kasar, domin ba a taba samun irin wannan sauye-sauye na bawa mata damarmaki a kasar ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng