An kama wani makiyayi da kansakalin harsashi (bullet-proof ) a jihar Benuwe
- Rundunar attisayen gudun muzuru sun kama wani makiyayi da kansakalin harsashi
- Kanal Aliyu Yusuf ya ce dakarun sojoji sun raba wata mumunar fada da ya so ya barke a tsakanin makiyaya da mafarauta a Benuwe
Rundunar sojin Najeriya sun kama wani makiyayi da kansakalin harsashi (Bullet Proof Vest) a kauyen Chegba dake karamar hukumar Logo a jihar Benuwe.
Kanal Aliyu Yusuf, ya ce sun mika mai laifin wanda suka kama shi tare da adda zuwa hanun jami’an ‘yansandan jihar Benuwe.
KanalYusufu, yace bayan haka dakarun sojoji su sun raba wata mumunar rikci da yaso ya barke a tsakanin makiyaya da masu farauta a karamar hukumar Obi bayan an sanar da su a waya.
KU KARANTA : 2019: Buhari ya riga ya sami kuri'u miliyan 12 - Don Etiebet
Yusuf ya kara da cewa, rundunar su dake gudanar da attisayen ‘Gudun muzuru’ sun kwato bidigogin hannu da harsashi a kauyen Gidan Kiya dake karamar hukumar Ibbi a jihar Taraba.
Yayi kuma yi kira ga mutanen yankin da dakarun su ke gudanar da ‘attisayen gudun muzuru’ da su cigaba da ba su hadin kai da kuma kai musu rahoton duk wani abu da suke zargin zai iya zama barazana ga zaman lafiyar yankin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng