Fitacciyar jaruman fina-finan Bollywood Sridevi ta mutu

Fitacciyar jaruman fina-finan Bollywood Sridevi ta mutu

- Allah yayi wa jarumar fina-finan Indiya mai suna Sridevi Kapoor rasuwa a ranar Asabar

- Sridevi Kapoor ta mutu ne a Dubai bayan sn je wani baki tare da mjin ta a Dubai

Shararriyar jarumar fina-finan Indiya na Bollywood Sridevi Kapoor, ta rasu a daren ranar Asabar sakamakon bugun zuciya a birnin Dubai.

Sanjay Kapoor, dan uwan mijin jarumar, ya sanar wa manema labarun kasar India mutuwar ta.

Sridevi Kapoor, ta mutu ne a Dubai bayan sun je wani biki tare da mijinta Boney Kapoor da diyar ta mai suna Khushi.

Fitacciyar jaruman fina-finan Bollywood Sridevi ta mutu
Fitacciyar jaruman fina-finan Bollywood Sridevi ta mutu

An haifi Sridevi ne a ranar 13 ga watan Augusta, 1963 a Tamil Nadu dake kasar Indiya. Ta mutu ta na da shekaru 55 a duniya.

KU KARANTA : Jaruman Indiya 10 mafi kyawun halitta

Fim dinta na farko da ta yi wato na Hindi shi ne fim din Solva Sawan wanda aka yi shi a shekarar 1979.

Sridevi Kapoor, tayi fina-finai fiye da 150 ciki har da wadanda da suka yi fice kamar, Mawali, Sadma, Mr India, Chandni, Nagin, Chalbaaz, Janbaaz, English Vinglish, Chandra Mukhi da kuma fim din ta na karshe mai suna Mom.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: