Siyasar Kano: Sanda na fara siyasa Kwankwaso yana makaranta - Ganduje

Siyasar Kano: Sanda na fara siyasa Kwankwaso yana makaranta - Ganduje

- Gabanin zabukan 2019, siyasar Kano ta zau zafi

- Ganduje da Kwankwaso sun babe tun 2015

- An ma zub da jini tsakanin mabiyansu

Siyasar Kano: Sanda na fara siyasa Kwankwaso yana makaranta - Ganduje
Siyasar Kano: Sanda na fara siyasa Kwankwaso yana makaranta - Ganduje

A ci gaba da ake da fafatawa, ta kalamai da makamai, tsakanin masoya da uwayen tafiyar Gandujiyya da Kwankwasiyya, Gwamna Ganduje ya sake baro ta, bayan da Kwankwaso ya kushe zabukan kananan hukumomi a matsayin dauki-dora.

Gwamnan ya mayar wa da Sanatan martani da cewa shi yaro ne, wanda bai ma san siyasa ba. A cewar Gwamna Ganduje dai, sa'ilin da ya shiga siyasa babu ko alamar Kwankwaso domin lokacin yana makaranta.

DUBA WANNAN: Matsalolin APC guda bakwai a yau

A hirarsa da jaridar Sun, Gwamna Ganduje ya kara da cewa, ga alama ko Tinubu ba zai iya sasanta su ba, domin sau 17 ana wannan kokari amma gwamnan yana tankwabar da kokarin dattijai.

Gwamna Ganduje yace, bama-bamai Kwankwaso ya biz-bizne masa gabanin mika masa mulki, kawai don a fadi, musamman basussuka da kudaden da ya san jihar baza ta iya biya ba.

"Ko Kudin makarantu da na 'yan kwangila sun kai Biliyan 300 na nairori, sannan kwatsam ma sai yace ilimi kyauta ne, kawai don ina na hana a ce na gaza."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: