Albishirin ku manoma: Kasashen Australia da Canada UAE su na bukatan doya 'yar Najeriya

Albishirin ku manoma: Kasashen Australia da Canada UAE su na bukatan doya 'yar Najeriya

- Doyan Najeriya ta samu karbuwa a kasashen Australia da Canada da UAE

- Amurka (USA) kadai, za a rinka kai ma ta doya ton 480 a kowace wata

- Ciyaman din Kwamitin Fitar da Doya zuwa Kasashe, Farfesa Simom Irtiwang, shi ne ya bayyana hakan

A yayin da Najeriya ta karkata zuwa habaka tattalin arzikin ta ga barin fitar da man fetur, Kasashen Canada da UAE da Australia sun bukaci a shigo ma su da doya daga Najeriya. Ciyaman din Kwamitin Bunkasa Fitar da Doya zuwa Kasashe, Farfesa Simon Irtiwang, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 21 ga watan Nuwamba.

Tirkashi! Kasashen Australia da Canada UAE su na bukatan doya 'yar Najeriya
Tirkashi! Kasashen Australia da Canada UAE su na bukatan doya 'yar Najeriya

Legit.ng ta tattaro bayanai na cewar Irtiwang ya ce neman da a ke wa doyan Najeriya ya yawaita tun fara fitar da shi zuwa Kasashe a 29 ga watan Yuni na 2017. Ya ce a wannan shakarar, za a rinka kai wa Amurka (USA), jimillar doya mai nauyi ton 480 a kowace wata.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda basu da ikon kama makiyayan da ke kiwo a filin jirgin sama - Kwamishina

Wannan baya ga neman doyar da a ke yi ne a kasashen Canada da UAE da Australia. Rahotonni sun nuna cewar yawaitan 'yan Najeriya a Israel ya sa a na matukar bukatar doya a can Kasar. Kwamitin ta na gudanar da bincike na kimiyya don samar da doya mai inganci.

Kwamitin za kuma ta tabbatar da doyan ya na dadewar akalla watanni 6 a ajiye kafin ya canja yanayi ko ya lalace. Don haka ne ta yi kira ga 'yan kasuwa ma su harkar da su hada kai da Gwamnati don tabbatar da sun samar da doya wanda zai samu karbuwa a kasashe.

A game da yuwuwan karancin doya a gida Najeriya kuwa, Farfesan ya ce hakan ba za ta faruwa ba, don kuwa manoma da dama sun dukufa ga noman doya a inda kuma suke samun tallafi daga hannun Gwamnati.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164