A yau ne aka bude wani katafaren masallacin Juma'a a garin Kontagora (hotuna)
- An bude wani katafaren masallaci a garin Kontagora
- Tsohon Sakataren mulkin soja na zamanin Abacha, Janar Seed mai Ritaya ne ya gina
- Ya kuma mallaka masallacin ga kungiyar Izala
Rahotanni sun kawo cewa a yau Juma’a, 23 ga watan Fabrairu, an kaddamar da wani sabon masallacin Juma’a a garin Kontagora dake jihar Niger.
Tsohon Sakataren mulkin soja na zamanin Abacha, Janar Seed mai Ritaya ne ya gina katafaren masallacin sannan ya mallaka shi ga kungiyar Izala karkashin shugabancin Bala Lau.
KU KARANTA KUMA: Gwamna Ganduje ya bayar da tallafin bargo 100,000 da kuma N20m ga yan gudun hijira a jihar Borno (hotuna)
A yau ne aka fara gudanar da Sallah a cikin masallacin inda gwamnan jihar ta Niger, Alhaji Abubakar Sani Bello ya halarta tare da sa albarka.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da tallafin bargon rufa guda 100,000 da kuma kudi naira miliyan 20 ga yan gudun hijira a jihar Borno.
Sannan kuma Ganduje ya dauki nauyin wasu yan gudun hijira 100 daga makarantar Firamare har zuwa matakin digiri a jihar Kano.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng