Rikicin jami’an gidan yari da yan daba: An rasa akalla rayuka 2

Rikicin jami’an gidan yari da yan daba: An rasa akalla rayuka 2

Hukumar yan sanda jihar Sokoto ta tabbatar da mutuwan mutane biyu da kuma jikkatan mutum daya sakamakon rikicin da ya barke tsakanin yan daba da jami’an gidan yari a jihar Sokoto.

Kakakin hukumar, ASP Cordelia Nwawe, ta ce wasu yan baranda sun kai hari kan wani motan jami’an gidan yari yayinda za’a gabatar da wasu fursunoni a kotu.

Nwawe ta bayyana cewa sun samu nasarar tsayar da motan a titin Sultan Abubakar kuma sukayi kokarin tsiratar da fursunonin.

Rikicin jami’an gidan yari da yan daba: An rasa akalla rayuka 2
Rikicin jami’an gidan yari da yan daba: An rasa akalla rayuka 2

Tace biyu daga cikin yan daban sun hallaka kuma daya ya jikkata. An nada wani mataimin kwamshanan ya gudanar da bincike cikin al’amarin.

KU KARANTA: Takaddamar tsakanin Tinubu da Oyegun: Muna bayan Oyegun - Gwamnonin APC

Amma an samu nasarar mayar da dukkan fursunonin 18 da aka fita da su gidan yari kuma an karfafar tsaro a gidan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng