Takaddamar tsakanin Tinubu da Oyegun: Muna bayan Oyegun - Gwamnonin APC
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa dukkan gwamnonin jam’iyyar All Progressive Congress, APC, na bayan shugaban jam’iyyar, John Odigie-Oyegun a kan takaddamar da ke tsakaninsa da Tinubu.
Gwamna Bello ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan ganawar da sukayi da shugaban kasa, Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa a daren jiya Alhamis, 22 ga watan Fabrairu, 2018.
Yayinda yake jawabin, Bello ya ce gwamnonin jam’iyyar sun amince da Oyegin duk da zargin sa babban jigon jam’iyyar, Ahmed Bola Tinubu, ke masa na cewa yana masa zagon kasa.
Yace: “Gwamnoni da mafi akasarin mambobin jam’iyyar APC sun amince da shugabanmi, Cif John Oyegin. Kana kuma mun amince da nada Bola Tinubu da shugaba Buhari yayi domin dinke barakar da ke cikin jam’iyyar.”
Zaku tuna cewa shugaba Buhari ya nada babban jigon jam’iyyar APC, Bola Ahed Tinubu a matsayin wanda ya hada kan ‘yayan jam’iyyar da ke rabe.
KU KARANTA: Olu na Warri ya ziyarci shugaba Buhari a fadar Villa
Amma daga fara aikinsa, Tinubu ya zargi shugaban jam’iyyar na kasa ba baki daya, John Oyegun, da yi masa zagon kasa a yunkurin aikin da aka sanya shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a: https://facebook.com/naijcomhausa https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng