NEF: Dattawan Arewa sun nada Farfesa Ango Abdullahi a matsayin Shugaban su
- Wata Kungiyar Dattawan Arewa ta nada sabon Shugaban ta
- Farfesa Ango Abdullahi ne zai ja ragamar wannan kungiyar
- An nada irin su Sani Zangon-Daura a cikin shugabannin NEF
Mun ji cewa Kungiyar Dattawan Arewa ta NEF ta nada Farfesa Ango Abdullahi a matsayin sabon Shugaban ta kuma shugaban kwamitin amintattu inda kuma su ka nemi a gyara harkar tsaro.
Mohammed Bello Kirfi wanda shi ne shugaban wani kwamiti na zartarwa na Kungiyar ya sanar da cewa sun yi wani taro na musamman a ranar Larabar nan a Garin Abuja inda su ka dauki mataki game da kungiyar da kuma halin da kasa ke ciki.
KU KARANTA: Shugaba Buhari zai gana da Gwamnoni a Fadar sa yau
Kirfi ya bayyana cewa bayan taron na Abuja ne su ka shirya nada wasu kwararru da za su jagoranci ragamar Kungiyar ta Arewa. Sauran wadanda aka nada su jagoranci kungiyar sun hada da Alhaji Sani Zangon-Daura a matsayin Mataimaki.
Sauran shugabannin Yankunan kasar sun hada da Yahaya Kwande da Janar Paul Tarfa. Akwai kwamitin lura da ya kunshi irin su Sam Nda Isiah, Hakeem Baba-Ahmed da sauran su. Kungiyar ta kuma nemi a kawo karshen rikicin Makiyaya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng