Wata Kotu a Gombe ta zartar ma wani makashin maza hukuncin kisa ta hanyar rataya
Wata babbar kotin jihar Gombe ta yanke ma wani matashi mai shekaru 37 hukuncin kisa ta hanyar rataya ko kuma ta hanyar yi masa allurer guba bayan ta kama shi da laifin kisa da fashi da makami.
Daily Trust ta ruwaito tun a shekarar 2014 ne aka gurfanar da dan fashin mai suna Suleiman Ibrahim a gaban Kotu, inda ake tuhumarsa da laifin kashe wani mutumi bayan ya yi masa fashi da makami.
KU KARANTA: Yan bindiga sun dira gonar wani attajiri, sun yi awon gaba da shanu ɗai ɗai har guda 95 a jihar Kogi
Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar 24 ga watan Nuwambar shekarar 2013 ne dai Suleiman ya dauki wani dan achaba ya kai shi zuwa kwalejin ilimin na gwamnatin tarayya dake Gombe, amma da isarsu sau ya fito da wani farin fauda, ya watsa ma dan achabar.
Nan take dan achabar ya kwanta sumamme, shi kuma barawon ya yi awon gaba da babur dinsa, inda daga bisani kuma dan achabar ya mutu a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya dake garin Gombe, kamar yadda lauya mai kara, Alhassan Mu’azu ya tabbatar ma Kotu.
Lauyan ya babyyana cewa lafin ya ci karo da sashi na 298 (c) na kundin hukunta manyan laifuka. sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin, amma duk da haka, hakan bai hana alkalin Kotun, Mai shari’a Beatrice Iliya yanke hukunci ba.
Bayan sauraron dukkan bangarorin mai kara da wanda ake kara, sai Mai shari’a Beatrice Iliya ta yanke ma wanda ake kara, Suleiman Ibrahim hukuncin kisa ta hanyar rataya ko kuma ta hanyar yi masa alluran guba, sa’annan ta umarci a mika babur din ga kanin dan achabar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng