Daidai ruwa, daidai tsaki: Jihohi guda 4 da suka fi biyan albashi mai tsoka ga ma’aikatansu
Binciken alkalumma daga hukumar kididdiga ta kasa ya nuna jihohin jihar legas, Ribas, Benuwe, Kogi da jihar Filato ne suka fi dukkanin jihohin Najeriya biyan albashi mafi daraja, kamar yadda Daily Trust ta gano.
Sai dai wani hanzari ba gudu ba, a yayin da jihohin Legas da Ribas suke hubbasa wajen tara makudan kudaden shiga a jihohinsu, su kuwa jihohin Benuwe, Kogi da Filato basu da wannan karfin arzikin, amma kuma sune kan gaba a biyan a albashi, hakan ne ma ya jefa su cikin matsalar kasa biyan albashi a bana.
KU KARANTA: Yan bindiga sun dira gonar wani attajiri, sun yi awon gaba da shanu ɗai ɗai har guda 95 a jihar Kogi
Majiyar Legit.ng ta ruwaito kowanne daga cikin jihohin uku basa tara kudin shiga da ya haura naira biliyan 10 a duk shekara, amma Benuwe na biyan albashin naira biliyan 94.8, Kogi biliyan 30, Filato kuma bilyan 20.4 a duk shekara, don haka basa iya cimma biyan albashin ma’aikata ba tare da ciyo basussuka ba.
Jihar Benuwe na biyan ma’aikaci da ya kai matsayin darakta N280,000, Kogi kuma na biyansa N230,172, yayin da jihar Filato ke biyansa N236,862. Ita kuma jihar Kano dake samun kudin shiga naira biliyan 30.96 a shekara tana biyan Darakta N150,00, jimilla tana biyan N110.4 biliyan a duk shekara ga ma’aikatanta 160,000.
A yayin da Ribas ke biyan darakta N285,000, inda take samu kudin shiga na N85.29 biliyan, a shekara, kuma take biyan kafatanin ma’aikatanta da suka kai 25,000, N100.8 biliyan, ita kuwa jihar Legas N347,733 take biyan darakta, tana samun N302.42 biliyan, tare da biyan ma’aikata 100,433 albashin N72 biliyan a shekara.
Majiyar ta cigaba da fadin, jihar Kaduna na biyan darakta N106,000, inda take kashe N26.4 biliyan akan biyan albashin ma’aikatanta su 100,000, kuma tana tara N17.5 biliyan kudin shiga. Jihar Katsina ita kuma na samun tara kudin shiga N5.5 biiyan, tana biyan darakta N150,174, inda jimillan ma’aikatanta su 39,775 ke lashe N60 biliyan a albashi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng