Yansandan sun cafke yan fashi 16 a yayin da wasu matasa suka hallaka wani gawurtaccen dan fashi
Wasu matasa sun lakada ma wani dan fashi da makami dukan tsiya a jihar Kano, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarsa har lahiram kamar yadda rundunar Yansandan jihar ta tabbatar.
Daily Trust ta ruwaito Kaakakin rundunar, DSP Magaji Musa Majia ne ya tabbatar da lamarin, inda yace matasan sun kashe wannan dan fashi ne yayin da ya tafi aikata fashi da makami a unguwar sharada.
KU KARANTA: Rikicin iyakan fili ya janyo ma wasu Yansanda guda 3 da wani jami’in Soja cin dukan tsiya a hannun fusatattun matasa
Majia ya bayyana sunan dan fashin, Bashiru Isah Adamu, kuma mazaunin titin mahauta ne, a can garin Bini na jihar Edo, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito shi, Kaakakin ya cigaba da fadin cewa da misalin karfe 4 na yammacin ranatr Litinin 19 ga watan Feburairu ne ya isa unguwar sharada, inda yayi basaja a matsayin ma’aikacin hukumar wutar lantark, KEDCO, tare da wani abokinsa da ya tsere.

A lokacin da suka kwankwasa wani gida, sai matar gidan ta fito, inda suka nemi ta nuna musu shaidar biyan kudin wutansu, komawarta gida keda wuya da nufin dauko musu takardar, sai suka bi ta ciki dauke da wuka, da wata karamar bindiga.
Nan da nan suka bukaci yar matar tare da mai aikinsu da su kwankwanta, kuma suka yi mata fashin kwamfutanta, na’aurar adana kayayyakin kamfuta guda biyu, Ipad, wayoyinta guda biyu da kuma tsabar kudi naira 8,000, har ma suka tilasta mata ta tura musu makudan kudi daga bankin ta zuwa nasu ta waya.
Sai dai a lokacin da suka yi kokarin fita daga gidan ne sai matar ta kwala ihu, wanda ya janyo hankalin makwabta, inda suka kama shi, guda kuma ya tsere. Kafin kace kule, sun daka masa wawa, tare da lakada masa duka har sai da yace ga garinku nan, tun ma kafin Yansanda sun hallara
A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jihar Kano ta sanar da kama wasu masu garkuwa da mutane guda biyu, da wasu yan fashi su 16 da suka addabi al’ummar jihar, inda ta yi bajakolinsu tare da nau’o’in makaman da suke dauke su.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng