Sojoji sunyi ajalin wata daliba bayan sun sa ta tsallen kwado saboda tayi lattin zuwa makaranta
Yan uwan Queendaline Ekezie, yarinya mai shekaru 15 wacce ta kasance daliba a makarantar sakandare na sojoji dake Obinze, Owerri, jihar Imo sun shiga mawuyacin hali bayan wasu sojoji biyu sunyi ajalinta sanadiyan wani mummunan horo da suka yi mata.
An rahoto cewa sojojin sun sa ta tsallen kwado bayan tai so makaranta a makare a ranar Alhamis.
An tattaro cewa dalibar wacce ta jigata bayan ta maimaita horon lokuta da dama, ta yanke jiki ta fadi.
An rahoto cewa an kaita wani asibitin sojoji cikin gaggawa inda anan ne ta cika.
A lokacin da mahaifinta ya samu labarin lamarin, a take ya yanke jiki ya fadi inda aka kais hi asibitin garin cikin gaggawa domin samun kulawar likita.
KU KARANTA KUMA: Harin Dapchi Attack: Buhari ya umurci ministoci 3 da su ziyarci Yobe
Majiyarmu ta Punch Matro ta kawo cewa Queendaline, wacce ke aji uku na karamar sakandare na tare da wata abokiyar karatunta, Delight Aguocha, dalibar aji biyu lokacin da abun ya afku.
Aguocha ta bayyana cewa horon mugunta da akayi masu shine ya kashe kawar tata.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci Ministan tsaro, Birgediya Janar Mansur Dan-Ali mai ritaya, Ministan bayanai, Lai Mohammed da kuma Ministan harkokin waje, Mista Geoffrey Onyeama da su ziyarci kauyen Dapchi dake Yobe domin duba yan matan makarantar da aka ce an sace.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng