Mai Rusau: El-Rufai ya bukaci jam'iyyar APC ta kalubalance shi a kotu
- Gwamna Jihar Kaduna ya bukaci jam'iyyar APC ta kalubalance shi a kotu, a dalilin rushe sakatariyar jam'iyyar da yayi
- Ya bayyana cewar yayi hakan akan doka da kuma bin ka'ida
- Ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi buris da maganganun da ake yi na rushe sakatariyar jam'iyyar APC da yasa aka yi a garin Kaduna. Ya ce gwamnatin sa tana aiki bisa bin doka da ka'ida ne, domin kawo cigaba da bunkasa jihar Kaduna.
DUBA WANNAN: Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin karbe makaman da suka sabawa doka
El-Rufai wanda ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, ya ce matakin da ya dauka yayi dai - dai domin bai sabawa abinda doka ta tsara ba.
Sannan ya shawarci wadanda abin bai yi musu dadi ba dasu kalubalance shi a kotu maimakon su dinga bin kafan yada labarai suna ta surutu. A cewar shi, gidan da yasa ka aka rushe dake kan hanyar 11B Sambo Road, gwamnatin jihar Kaduna tana bin shi haraji na sama da shekaru 8.
An rushe sakatariyar jam'iyyar APC dinne a ranar Talatar nan, kwana biyu bayan jam'iyyar mai mulki ta dakatar da gwamnan na tsawon wata shida, saboda zargin da take yi mashi na cin zarafin al'umma.
Sai dai gwamnatin jihar Kadunan ta ce yanzu haka ta mai da filin sakatariyar wurin shakatawa.
Gwamnan wanda yayi magana ta hanyar babban mai bashi shawara game da harkokin siyasa, Malam Uba Sani, ya ce gwamnati ta bi hanyar da ta dace wurin rushe wuraren, sannan kuma gwamnati ta gargade su kafin ta dauki matakin rushe wuraren.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng