Mutane 156 ne zasu kara a gasar Al-Qur’ani na kasa a Katsina

Mutane 156 ne zasu kara a gasar Al-Qur’ani na kasa a Katsina

Kimanin mutane 156 daga jihohi 32 da kuma birnin tarayya ne zasu kara a gasar karatun Al-Qur’ani na kasa karo na 32 wanda za a gudanar a jihar Katsina daga ranar 23 ga watan Fabrairu zuwa 3 ga watan Maris na wannan shekarar.

Shugaban kungiyar dake shirya gasar, Justis Musa Danladi Abubakar ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a jiya Laraba, 21 ga watan Fabrairu.

Ya bayyana cewa an kammala duk wani shiri domin gabatar da wannan taro.

Mutane 156 ne zasu kara a gasar Al-Qur’ani na kasa a Katsina
Mutane 156 ne zasu kara a gasar Al-Qur’ani na kasa a Katsina

Ya ce, abubuwan da aka ajiye ga za a ba wanda yayi nasara sun hada da kujerar makkah, Babura, da kuma kudade inda ya bayyana cewa musababbin wannan gasa shine domin a sanya al’adan karanta Qur’ani a zukatan yara masu tasowa.

KU KARANTA KUMA: Harin Dapchi Attack: Buhari ya umurci ministoci 3 da su ziyarci Yobe

ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar zata bayar da tallafinta yadda ya kamata wajen gabatar da taron yayinda zuwa yanzu an zuba sama da naira miliyan 119 domin ganin yadda abun zai kama bayan an fara taron.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: