Garin gaidam na cike da farin ciki yayin da aka tarbi 'yan makaranta da sojoji suka ceto
- Soji sun maido da 'yammatan garin Gaidam 'yan makaranta da su ka kubutar
- Daukacin mutanen garin sun fito cike da farin ciki don tarban 'yammatan
- Dokar takaita yawo a garin bai hana mutanen garin fitowa tarban 'yammatan ba
Mutanen Gaidam sun bijirewa dokar takaita yawo na karfe 9 na dare a garin, sun fito cike da murna da farin ciki don tarban 'yammatan garin 'yan makaranta da a ka kubutar.
Jaridar Daily Trust ta tattaro bayanai cewar manya da yara da tsaffi da matan aure sun yi dafifi a kan titin Maine-Sorroa, inda a nan ne su ka tarbi 'yammatan cike da farin ciki.
Su kuma samari matasa sai wasa su ke kan kekuna cike da murna, su na fadin 'gari ya waye'. Wani mutumi mai suna Malam Usman Kura, ya bayyana cewar shekaru 3 kenan rabon sa da fitowa gida a irin wannan lokaci
DUBA WANNAN: Cuwa-cuwan kudi na N13.6bn: Kotu ta dage shari'ar Dasuki zuwa 22 ga watan Maris
Kasancewar 'yammatan sun kubuta daga hannun 'yan ta'adda, ya ce dole ne kuwa shi da iyalin sa su fito don yin murna da shaida wannan lokaci na farin ciki.
Rundunar Soji da Mafarauta ne su ka yi wa 'yammatan rakiya a jerin motoci zuwa Barikin Soja da ke garin, da daren ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng