Wani karamin Soja ya budawa babban Jami’in Soja wuta a filin yaki
- Wani karamin Soja ya sakarwa kyaftin din Sojan Najeriya harsashi
- Yanzu haka dai an wuce da wannan babban Soja zuwa asibitin Sojoji
- Wasu na ganin dai takaicin yaki ne ya kan jawo kurata su buda wuta
Mun samu wani labari mai ban takaici daga Jaridar Cable cewa wani karamin Sojan kasar nan ya harbi mai gidan sa wanda yake Kyaftin a Garin Banki a cikin Jihar Borno a Ranar Lahadin da ya wuce da kimanin karfe 9:13 na dare.
Yanzu haka majiyar ta Jaridar The Cable tace an wuce da Sojan zuwa asibitin Sojoji da ke yankin. Shi kuma wannan Soja da yayi wannan tabargaza yana tsare a hannun manyan sa bayan an karbe kayan bindigar da ke hannun sa.
KU KARANTA: 'Yan Sanda sun damke wasu da laifin kisan 'Dalibar Jami'a
Lambar wannan kofur na Soja mai suna Peter Omobuwa dai ita ce N/12897 yayin da kuma babban Jami’in da aka buda wuta yake da 02NA/52/2588. Za a nada kwamiti da za su yi binciken hukuncin da za a daukan kan wannan Soja.
Ba dai yau aka fara samun irin wannan rikici ba don kuwa ko a bara wani Sajan mai suna Silas Ninyo ya kashe wani Kyaftin T, Mani har kuma daga karshe wannan karamin Soja ya kashe kan sa saboda fushi da takaicin yaki.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng