Za a yi zazzaga a Hukumar JAMB bayan an bankado badakaloli

Za a yi zazzaga a Hukumar JAMB bayan an bankado badakaloli

- Binciken da aka gudanar a Hukumar JAMB zai sa wasu rasa aikin su

- An samu wasu da laifin sace makudan miliyoyi na Hukumar kwanaki

- Mai magana da bakin Hukumar yace ana iya korar wannan Ma’aikata

Bisa dukkan alamu binciken da aka yi a Hukumar JAMB ta kai za a sallami ma’aikatan da aka samu da laifi. Akwai wadanda aka samu da laifin karkatar da dukiyar Hukumar zuwa alijihun su kuma za su iya rasa aikin su inji mai magana da yawun Hukumar.

Za a yi zazzaga a Hukumar JAMB bayan an bankado badakaloli
Shugaban Hukumar jarrabawa ta JAMB

Daily Trust ta bayyana cewa ana shirin korar Ma’aikatan JAMB da aka samu da laifin satar kudin da aka samu ta hanyar saida katin jarrabawa a Jihohi da dama na Hukumar. Shugaban na JAMB Farfesa Ishaq Oloyede da gaske yake yi na kawo gyara a Hukumar Kasar.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta samu makudan kudi daga hannun barayin Gwamnati

Binciken da aka yi kwanakin baya ya nuna cewa akwai masu hannu dumu-dumu wajen satar kudin da ya kamata ace ya shiga hannun Gwamnati inda wasu Ma’aikata su ka rika bada uzurin da ba su samu karbuwa ba. Akwai inda ma aka ce maciji ne ya hadiye kudin.

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bada umarni ayi bincike wasu Hukumomin Gwamnati wanda su ka hada da JAMB. Kwanaki aka ta jin yadda aka rika tafka badakala a hukumar a Garuruwan Benuwe, Yobe, Kano. Gombe da sauran su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng