An gurfanar da Al-Barnawi, shugaban 'Yan Ansaru, a gaban kotu a Abuja
- An gurfanar da babban dan ta'addan nan Al-Barnawi a babban kotu a Abuja
-Al-Barnawi shine shugaban kungiyar nan ta Jama'atu Ansarul Musulimina fi biladil Sudan
- A shekarar 2012 kasar Amurka ta ce zata bada tukwici ga duk wanda ya taimaka aka kama shi
A ranar Alhamis dinnan ne data gabata aka gurfanar Khalid al-Barnawi, shugaban kungiyar nan ta Jama'atu Ansarul Musulimina fi biladil Sudan, wadda ta cire kanta daga cikin kungiyar Boko Haram, a gaban wata babbar kotu a babban birnin tarayya Abuja.
DUBA WANNAN: An ceto matan da Boko Haram suka sace a Yobe
Kotu tana tuhumar sa tare da wasu mutum bakwai da aikata laifukan ta'addanci da suka hada da sata da kuma yin garkuwa da wasu Turawa da Larabawa 'yan kasashen waje, da suka samu nasarar kama su a yakin jihar Bauchi, jihar Kebbi da kuma jihar Kano daga shekarar 2011 zuwa shekarar 2013, inda daga baya suka kashe su.
Wadanda ake zargin sun musanta zargin da ake yi musu, yayin da aka daga sauraren karar tasu zuwa watan Afrilu.
A shekarar data gabata ma haka ta faru inda wanda ake zargin yayi watsi da zargin da ake yi masa. Sojojin Najeriya sun samu damar kama Al-Barnawi a shekarar 2016 a jihar Kogi.
Kasar Amurka ta bada tabbacin bada tukwicin dala miliyan biyar ga duk wani wanda ya taimaka wurin kamo shugaban 'yan ta'addan.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng