Gwamnati zata kawo jirgin kasa na zamani daga Badun zuwa Kaduna

Gwamnati zata kawo jirgin kasa na zamani daga Badun zuwa Kaduna

- Ana zamanantar da tashoshin sufuri a Najeriya

- An maida hankali kan hanyoyin jiragen kasa

- Za'a kawo sabon layin dogo Arewa daga kudu

Gwamnati zata kawo jirgin kasa na zamani daga Badun zuwa Kaduna
Gwamnati zata kawo jirgin kasa na zamani daga Badun zuwa Kaduna

A taron majalisar kasa na yau laraba, na wannan makon, shugaba Buhari ya zartas da kudurin kashe dala biliyan shida da miliyan dari bakwai {N6.7 billion dollars), domin a gina sabon layin dogo na zamani, wanda zai taso tun daga kudancin kasar nan, zuwa Kadunan Najeriya.

Layin dogon, wanda ake kira standard rail gauge, shine wanda ake amfani dashi a duniya baki daya, wanda ke iya daukar kowanne irin jirgi kuma yake da matukar gudu.

DUBA WANNAN: An ceto matan da Boko Harm ta sace

Hadimin shugaban, kan hanyoyin sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, shine ya saki bayanan, inda yace shugaban na fata wannan aiki zai kawo ci gaba da zamanancewa ga yankunan da aikin zai shiga.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng