Da dumi-dumi: Soji sun ceto yan matan Dapchi da Boko Haram suka sace - Rahoto
Majiyar jaridar RFI da yammacin nan na nuna cewa dakarun sojin Najeriya sun shiga dajin da aka shiga da yan matan makarantan Dapchi kuma sun fito tare da wasu yan mata zuwa garin Dapchin.
Ana kyautata zaton cewa yan Boko Haram din sunyi garkuwa da yan mata akalla 60 a harin da suka kai ranan Litinin.
Har yanzu dai hukumar soji ko na yan sanda basu tabbatar da wannan labari ba.
Zaku tuna cewa mun kawo mukur rahoton Kwamishanan yan sandan jihar Yobe, AbdulMalik Sumonu, inda ya bayyana cewa babu wanda aka kashe kuma babu yar makarantan da yan Boko Haram suka sace a harin da suka kai makarantan yan matan garin Dapchi.
KU KARANTA: APC ta yi kira da hafson rundunar sojin Najeriya ya dakatar da GOC na 1DIV daga bakin aikin sa
Sumonu ya bayyanawa manema labarai a jihar Yobe cewa yan Boko Haram din sun yi garkuwa da maza 3 a karamar hukumar Geidam bayan harin Dapchi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng