Kotu ta karbi koken wani magidanci, bayan da saurayin matarsa yayi mata ciki
- Ismaila ya ce matar tasa tayi ciki ne da kwarton saurayinta
- Amina tace zargin banza yake yi mata, ita bata da kowa sai shi mijinta
- An sanya batun nasu a tsarin tuhuma domin fara musu sulhu kafin sharia
Wani magidanci, dan shekaru 34, Ola Ismaila, a jihar Legas, ya kai matarsa Aminatu kotu, bisa zargin ta da cin amanar aurensu inda wai tayi cii daga soyayyar da take da wani kwarto, saurayinta, inda yake rokon kutu ta warware musu suren su.
Aminatu dai, ta musanta zargin, inda tace ita babu wani namiji a rayuwarta sai shi mijin nata amma shi ya fiye mita da mugun zargi wanda bai da tushe balle makama.
DUBA WANNAN: Dalilan da suka hana 'yan kasuwa sayen man fetur da shigo dashi
Kotu dai a jihar Legas, ta umarce su da su je bayan kanta suyi kokarin yin sulhu, in kuma abin ya gaza, su dawo domin ayi musu sharia.
Aure dai ana sa rai soyayya ke hada shi, amma wasu mazan sukan ci amanar aure, wasu lokutan kuma, mata ke cin wannan amanar, sai dai an fi zuzuta na matan, inda aka dauki na mazan kamar ado ko ba-sabam-ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng