Iyaye na tururuwa domin kwashe 'ya'yan su daga makarantar mata da aka kai hari a Yobe
- Kungiyar Boko Haram ta kai wani hari a makarantar sakandiren 'yan mata dake Dapchi a jihar Yobe
- Rahotanni sun bayyana cewar kimanin 'yan mata 94 sun bace bayan harin
- Duk da hukumar 'yan sandan Najeriya ta karyata bacewar koda yarinya daya daga makarantar, iyayen yara na tururuwar kwashe'ya'yan su daga makarantar
A ranar Litinin ne 'yan kungiyar Boko Haram suka kai hari wata makarantar sakandiren 'yan mata dake garin Dapchi a jihar Yobe.
Rahotanni sun bayyana cewar a kalla 'yan mata 94 sun bace bayan kai harin.
Duk da hukumar 'yan sandan Najeriya ta karyata maganar batan yarinyar koda daya daga cikin daliban makarantar, iyayen yara na cigaba da tururuwar zuwa kwashe 'ya'yan su, kamar yadda jaridar TheCable ta wallafa.
Wani malami a makarantar, Muhammad Ismaila, ya shaidawa TheCable din cewar mafi yawan dalibai da malaman makarantar sun gudu ya zuwa makobtan kauyuka, sai dai ya ce ba zai iya tabbatar da cewar an sace wasu daga cikin daliban ba.
"Wasu daga cikin mu sun yi gudu kilomita 15 zuwa 25 domin tsira da ran su. Wasu daga cikin daliban mu 1,000 dake makarantar sun fara dawowa, wasu kuma har yanzu ana neman inda suka shiga," a cewar Isma'ila.
KARANTA WANNAN: Malamin makaranta ya bulale wani dalibi har lahira a Zamfara
Wani uba, Babagana Gujba, dake da diya a makarantar ya ce ya dauke 'yar sa ne daga makarantar saboda dalilan tsaro, tare da bayyana cewar ba zai bari rayuwar 'yar sa ta shiga hadari ba.
Kazalika wata daliba, Aisha Kachalla, da ta dawo makarantar ta bayyana cewar ba zata iya zama a makarantar ba saboda ta matukar tsorata da abinda ya faru.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng