Sojoji sunyi caraf da wata bindiga da ake talla, dillalai sun tsere

Sojoji sunyi caraf da wata bindiga da ake talla, dillalai sun tsere

- Dakarun sojin Najeriya sun gano wata kasuwar makamai a jihar Taraba

- Sojin sunyi nasarar kwato wata bindiga da aka tallata ta a baya

- Hukumar Sojin tayi kira ga al'umman yankunan da ake gudanar da atisayen su cigaba da bayar da hadin kai

Dakarun Sojin Najeriya na Briged 13 da ke gudanar da atisayen 'Ayem Akpatuma' wato Tseren Mage da ke yankin Bantaje na karamar hukumar Wukari da ke jihar Taraba sunyi nasarar gano wata bindiga a yayin da suke zagaye a ranar Talata 20 ga watan Fabrairun 2018.

Asirin wasu dilalan bindiga ya tonu yayin da Sojin Najeriya suka gano su
Asirin wasu dilalan bindiga ya tonu yayin da Sojin Najeriya suka gano su

Binciken da aka gudanar a baya ya nuna cewa an tallata bindigar a wani kasuwan bayan fage da dilalan bindiga ke siyar wa batagari makamai sai dai dilalan sun tsere yayin da suka hango sojojin na zuwa kamar yadda jami'an hulda da jama'a na rundunar SK Usman ya bayyana.

KU KARANTA: Majalisar Wakilai sunyi watsi da bukatar ware wa makiyaya filin kiwo, sun bayar da sabuwar maslaha

A halin yanzu dai ana cigaba da neman mutanen da ke da hannu cikin cinikin makamai wanda suke boye a yankin na Bantaje.

Hukumar Sojin na Najeriya tayi kira ga al'ummar da ke zaune a garuruwan da ake gudanar da atsayen na Tseren Mage su cigaba da bayar da hadin kai ga jami'an tsaro ta hanyar basu bayannai masu amfani da ka iya sa a gano battagarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164