Malaman makaranta sun kai gwamnatin jihar Kaduna kara gaban Majalisar Dattawa

Malaman makaranta sun kai gwamnatin jihar Kaduna kara gaban Majalisar Dattawa

- Malaman makaranta a jihar Kaduna sunyi korafi gaban majalisar dattawa game da rashin biyan su albashi

- Sanata Shehu Sani mai wakiltar yankin Kaduna ta tsakiya ne ya gabatar da kudirin a gaban majalisa

- Malaman makarantan dai sun dade suna dauki ba dadi da gwamnatin jihar tun bayan da aka sallame malamai 22,000 da suka fadi jarabawar cancanta

Kungiyan malamai na kasa (NUT) reshen jihar Kaduna sun gabatar wa Majalisar Dattawa da kudirin koke game da yadda gwamnatin jihar Kaduna taki biyan su hakokin su na albashi.

Sanata Shehu Sani mai wakiltan Kaduna ta tsakiya ne ya gabatar da kudirin a gaban majalisa a Laraba 21 ga watan Fabrairun 2018 a madadin kungiyar malaman reshen jihar Kaduna.

DUBA WANNAN: Rigingimun jam'iyyar APC: Rikici 6 da zasu yiwa Tinubu wuyar warwarewa

Gwamnatin jihar kadunan karkashin jagorancin gwamna Nasir El-Rufai dai sun dade sun dauki ba dadi da kungiyar malaman makarantar. Rikicin ya samo asalin ne tun lokacin da gwamnatin jihar ta bayyana cewa zata kori malamai 22,000 da suka fadi jarabawar cacanta.

A baya Legit.ng ta kawo muku rahoton inda gwamnatin na jihar Kaduna ta bayyana cewa ta fara tantacewa da rabar da takardun fara aiki ga sabbin malamai 22,000 da ta dauka don maye gurbin wanda aka kora.

Gwamnatin jihar Kadunan ta bayyana cewa ta gudanar da jarabawar cancantar don tsamo fanin ilimi daga cikin halin ha'ula'i da ya shiga kamar yadda Hukumar kul da ilimin Frimare (SUBEB) na jihar ta fada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel