Malamin makaranta ya bulale wani dalibi har lahira a Zamfara

Malamin makaranta ya bulale wani dalibi har lahira a Zamfara

- Wani Malami a wata makarantar sakandire dake Sankalawa a karamar hukumar Bungudu ya kashe dalibinsa

- Mataimakin shugaban majalisar jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Abubakar Gumi, ya sanar da haka rana Laraba

- Ya bayyana cewar, ko a wata makarantar mata dake kwatarkwashi saida mataimakin shugaban makarantar ya raunata wata daliba da dukan da ya wuce kima

Wani malami a makarantar sakandiren garin Sankalawa a karamar Bungudu dake jihar Zamfara ya hallaka dalibin sa da duka.

Mataimakin shugaban majalisar jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Abubakar Gumi, ya sanar da hakan ranar Laraba.

Gumi ya gabatar da maganar ga majalisar ne yayin tattaunawa batutuwan dake bukatar duba na gaggawa yayin zaman majalisar a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Malamin makaranta ya bulale wani dalibi har lahira a Zamfara
Malamin makaranta ya bulale wani dalibi har lahira a Zamfara

A cewar Gumi, majalisar ta samu wani korafin mai kama da wannan, inda mataimakin shugaban makarantar mata ta kwatarkwashi ya raunata wata daliba saboda dukan da ya wuce kima.

KARANTA WANNAN: Tuna baya: Hotuna daga bikin fitaccen mawaki Fela lokacin da auri 27 lokaci daya

Shugaban majalisar, Alhaji Sanusi Rakiji, ya umarci kwamitin majalisar a kan ilimi su binciki al'amarin tare da daukan alkawarin hukunta duk malamin da aka samu da laifin cin mutuncin dalibai.

Kazalika majalisar ta gayyaci kwamishinan ilimin jihar ya bayyana a gaban ta domin amsa tambayoyi a kan zarge-zargen cin mutuncin dalibai.

Majalisar jihar ta amince da wani kudiri na gina jami'ar jihar a Talata-Mafara.Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng