An sake kwatawa: Akalla yan mata 94 sun yi ɓatan dabo tun bayan harin da Boko Haram ta kai makarantarsu a jihar Yobe

An sake kwatawa: Akalla yan mata 94 sun yi ɓatan dabo tun bayan harin da Boko Haram ta kai makarantarsu a jihar Yobe

Akalla dalibai yan mata 94 ne suka yi batan dabo tun bayan wani hari da yan ta’addan Boko Haram suka kai a kwalejin yan mata dake garin Dapchi, cikin karamar hukumar Busari a jihar Yobe.

Iyaye da malaman makarantar ne suka tabbatar da batar adadin daliban da a yanzu ba’a san halin da suke ciki ba, ko kuma inda suke ba, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

KU KARANTA: Kiri da muzu: Gwamna El-Rufai ya nesanta kansa da batun rushe gidan Sanata Hunkuyi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito da misalin karfe 7 na daren ranar litinin 19 ga watan Feburairu ne yan ta’addan suka far ma kwalejin yan matan, cikin motocin yaki guda 18, kuma har an gano gawawwakin dalibai hudu a cikin daji.

An sake kwatawa: Akalla yan mata 94 sun yi ɓatan dabo tun bayan harin da Boko Haram ta kai makarantarsu a jihar Yobe
Daliban yayin kidaya

A sakamakon harbe harben da yan ta’addan suka yi, dayawa daga cikin dalibai da malamansu sun shige cikin daji da nufin tsira da ransu, hakan ne ya sanya ba’a tantance adadin wadanda suka bata ba sai a ranar Talata, inda aka yi kidayan daliban da ke cikin makarantar.

Sai dai wani mazaunin garin Dapchi ya shaida ma majiyarmu cewa da alama yan Boko Haram sun dade suna shirya wannan hari, inda yace kimanin sati daya kenan daya gabata aka kwashe Sojojin dake gadin garin, wanda hakan ya baiwa yan ta’addan damar kai harin ba tare da wata matsala ba.

An sake kwatawa: Akalla yan mata 94 sun yi ɓatan dabo tun bayan harin da Boko Haram ta kai makarantarsu a jihar Yobe
Kayansu

Har sai bayan da yan ta’addan suka kammala ta’asar da suka yi a kwalejin yan matan ne sai ga Sojoji cikin motocin yaki da jiragen sama masu tashin angulu sun nufo makarantar, ba tare da samun nasarar cimma yan ta’addan ba.

Idan za’a tuna a watan Afrilun shekarar 2014 ne yan Boko Haram suka sace dalibai mata 270 dake karatun a kwalejin sakandarin yan mata dake garin Chibok, inda sai a shekarar 2017 ne gwamatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amso mata 100 daga cikinsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng