Kwalejin ilimi ta jihar Bauchi zata sanya ƙafar wando ɗaya da mata masu shigar banza
Hukumar gudanarwa ta kwalejin ilimi ta jihar Bauchi, dake garin Kangare sun sanar da haramta sanya wandunan masu matse jiki, da kuma gajerun siket ga dalibai mata, inji rahoton The Cable.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban kwalejin, Garba Kirfi ya bayyana cewa sun lura dalibai mata sun shiga halin sanya kayan banza, don haka ne ta haramta ma daliban kwalejin sanya gajerun siket, matsatstsun wanduna, kananan riguna da ire irensu.
KU KARANTA: Tsautsayi baya wuce ranarsa: Wasu ýan mata Uku sun yi asarar rayukansu sakamakon kulle kansu a cikin wata mota
“Mun nemi goyon bayan jama’an garin Kangare da su taimaka mana a kokarin da muke yi na magance matsalar shigar banza, don tun daga bakin gate zamu hana duk dalibar da ta yi shigar banza shiga kwalejin.
“Hakazalika muna aiki kafada kafada da kungiyoyin addinai da na dalibai don wayar da kan dalibai game da shigar banza, nan bada dadewa ba zamu fitar da tsarin shigar da muke bukata daliban kwalejin su dinga yi.” Inji shi.
Daga karshe malam Garba yace an umarci dukkanin shuwagabannin tsangayoyin ilimin kwalejin da su dabbaka dokar haramta shigar banza a ko ina a cikin makarantar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng