Mai ba Gwamna Ayade shawara ya ajiye matsayin sa ya koma APC
- Mai ba Gwamnan Kuros-Ribas shawara ya bar Jam’iyyar PDP
- Kila Jesse Williams zai yi takarar kujerar ‘Dan Majalisa a APC
- Jam’iyyar adawar tayi babban asara cikin ‘yan kwanakin nan
Dazu mu ka samu labari daga Premium Times cewa wani mai ba Gwamnan Jihar Kuros-Riba watau Ben Ayade shawara ya ajiye matsayin sa a Gwamnatin ya kuma tattara ya koma Jam’iyyar APC mai mulki.
Mai ba Gwamna Ayade shawara kan harkokin samawa matasa aikin yi Jesse William ya bar mukamin sa bayan ya bar Jam’iyyar PDP. William ya koma Jam’iyyar APC ne bayan yayi murabus daga matsayin da ya ke rike da shi.
KU KARANTA: Rikicin cikin gidan APC na sake zani a Najeriya
Jesse William ya tattara ya bar aiki da Gwamna Ben Ayade ba tare da wani batan lokaci ba inda ya aika wasika ga Shugaban Jam’iyyar PDP na Karamar Hukumar Biase. William ya fito ne daga Yankin Agwagune/Okuri, Agwagune.
Bisa dukkan alamu dai William ya fice ne daga PDP zuwa APC yayi takarar kujerar ‘Dan Majalisar Tarayya. Wasu na ganin idan PDP tayi sake za ta iya rasa Jihar a zaben 2019 saboda rashin da tayi cikin kwanakin nan zuwa Jam’iyyar APC.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng